<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Bari nufin Mai Cetona ya bishe ni koyaushe.
 Da ƙaunarsa da ikonsa su mallake ni.

[V2]
 2) Kalmarsa ta zauna kullum cikin zuciyata sosai,
 Don a rinjayi mugunta, sai ta ikonsa.

[V3]
 3) Salamar Allah Uban ta kiyaye duk raina,
 Don in ta'azantar da su masu ƃacin rai.

[V4]
 4) Ƙaunar Yesu ta cika ni kamar cikowar teku,
 Ya ɗaukaka, in ƙasƙanta, nasara ke nan.

[V5]
 5) Tsere gaba gaɗi zan yi, in tasar wa maƙiya,
 Yesu shi zan duba kawai, cin gaba zan yi.

[V6]
 6) Jamalinsa ya haskaka loton neman ƃatattu,
 Sanadin kuwa kar su damu, sai su gaskata.</lyrics>
<title>Bari nufin Mai Cetona Ya Bishe Ni Koyaushe LW237</title>
<hymn_number>237</hymn_number>
</song>